Kun san abubuwan da suka faru a Nigeria a makon jiya?

Wasu zababbun hotunan abubuwan da suka faru a Najeriya makon da ya gabata

A ranar Talata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da daya daga cikin manyan gonakin kiwon kaji a Afirka wacce aka gina a jihar Kaduna.
Bayanan hoto,

A ranar Talata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da daya daga cikin manyan gonakin kiwon kaji a Afirka wacce aka gina a jihar Kaduna.

Bayanan hoto,

Kamfanin Olam ne ya gina gonar wacce ake sa ran samunta zai rage shigar da kaji da dangogin su daga kasashen ketare.

Bayanan hoto,

A ranar Litinin ne Hukumar hana fasa kauri ta Najeriya, kwastam, mai kula da shiyyar tashar jiragen ruwa ta Tincan Island da ke a Legas a kudancin kasar, ta kama manyan bindigogi sama da dubu daya.

Bayanan hoto,

Ko wacce daya tana iya hallaka mutane da dama a cikin lokaci guda.

Bayanan hoto,

A ranar Laraba ne wasu dumbin mata daga Kungiyar 'yan uwa Musulmi wadda aka fi sani da Shi'a a Nigeria, suka bukaci hukumomi a kasar da su gaggauta sakin Shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Bayanan hoto,

A ranar Laraba ne wasu sarakunan gargajiya na arewa tare da wasu gwamnonin arewa suka yi taron sauya fasalin kasa a Kaduna.

Bayanan hoto,

Sarakuna da dama ne suka samu damar halartan taron, ciki har da sarkin Kano Muhammad Sanusi

Bayanan hoto,

Ko wacce daga cikinsu an danka mata akwati guda cike da sutura da sauran kayan amfani

Bayanan hoto,

Gwamnatin wacce ta shiryawa 'yan matan da kuma iyayensu lafiyar cin abincin dare a ranar Laraba a Abuja, ta ce sai da aka kwantarwa da 'yan matan hankali tare da duba lafiyarsu, a wani shiri na maido da su cikin hayyacinsu da gyara dabi'unsu da gwamnati ta shirya, kafin mayar da su a hannun iyayensu.

Bayanan hoto,

A ranar Alhamis ne matasa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya suka rungumi wani shirin dashen itatuwa da ake yi a wasu unguwannin birnin ta hanyar la`akari da sunayensu.

Bayanan hoto,

Manufar shirin it ace kwadaita wa al`uma raya itatuwan da irin na gargajiya da aka saba da su, wadanda masana ke cewa sun fi bakin itatuwa fa`ida ga al`umar yankin.