Komai zai iya faruwa a karawarmu da Arsenal — Conte

Komai zai iya faruwa a karawarmu da Arsenal- Conte
Bayanan hoto,

Komai zai iya faruwa a karawarmu da Arsenal- Conte

Kocin Chelsea Antonio Conte ya ce zai yi kokari ya yanke shawarar da ta dace a kan ko wanne wasa da kuma yin kokarin samun nasara.

"Kar ku manta samun nasara na da matukar muhimmanci a wurinmu. Ina farin -ciki da yadda 'yan wasanmu suke kokari bayan da muka kara da Qarabag. Yanzu kuma akawai babban wasan da zamu kara da Arsenal."

"Ya kamata mu tabbatar da lafiyar dukkkanin 'yan wasanmu, kuma zan yi kokari mu shirya sosai don tunkarar wasannin da suke gabanmu."

Ya kara da cewa, "Ina ganin Arsenal na daya daga cikin manyan kulob shida a Ingila, kuma sun iya buga wasa sosai, saboda haka za mu kara da kungiya mai muhimmanci.

"Bisa wannnan dalilai nake ganin wannan wani kalubale ne a garemu. Buga tamaula da Arsenal daya ne da fafatawa da Man city, da Liverpool, da Man United ko Tottenham."

Conte ya kuma ce komai zai iya faruwa, don haka za su fafata kuma za su dage wajen fafatawa da abokiyar adawarsu.