Rashin Pogba babban cikas ne — Mourinho

Pogba zai yi jinyar mako shida

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Pogba zai yi jinyar mako shida

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce, za su yi kewar Pogba domin suna bukatarsa.

"Sai dai Ander Herrera, da Marouane Fellaini da Michael Carrick na jiran amfani da damar. A baya ma mun yi rashin 'yan wasa a lokaci mai muhimmanci. Amma ba muyi takaici ba," in ji shi.

A ranar Lahadi ne United za ta karbi bakuncin Everton, tare da tsohon kyaftin dinta Wayne Rooney, wannan ne karon farko da Rooney za su kara da United tun bayan barinsa Old Trafford.

"Za mu yi masa maraba saboda ya cancanta," in ji shi.

Ya kara da cewa, "A wasu lokutan kalmar labari na da saukin samu a Ingila, amma ba a irin wannan yanayin ba, na lashe kofuna da cin kwallaye.

"Yana daya daga cikin 'yan wasa masu matukar muhimmanci a United. Kuma filin wasan zai karramashi da ba shi girma domin ya cancanta."