Nigeria: Jirgin ruwa ya kife da mutum 150 a Kebbi

Kwale-kwale

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Laraba ne kwale-kwale ɗauke da 'yan kasuwa 150 daga kauyen Gaya cikin jamhuriyar Nijar da ke kan hanyar zuwa kasuwa a garin Lolo a jihar Kebbi ya kife.

An samu ceto mutane 50 daga cikinsu. Har yanzu ma'aitakan ceto daga jamhuriyyar Nijar da Najeriya na ci gaba da aikin ceton waɗanda suka rage. Sai dai babu tabbas cewa za'a same su a raye.

A halin yanzu an kai wadanda aka ceto asibitin Lolo domin samun magunguna da kulawa.

Jami'an hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Sokoto, Suleiman Mohammed Kasim ya ce suna kokarin shawo kan lamarin.

"Idan abu ya faru kamar haka, Hukumar NEMA ta kan turo jami'ai wadanda suka kware wajen ceto mutane. Da wannan abu ya faru an samu hadin kai ma'aikatan ceto na gargagiya domin ceto wadanda suka bata," in ji shi.

Ya kara da cewa, "Mutane da yawa na yin cunkoso a cikin jirgin ruwan da ke daukar mutum 70 zuwa 100, inda za ka ga an dauki mutane 150 har ma da kayayyaki.

Suleiman Mohammed ya ce a nan gaba hukumar NEMA za ta wayar wa da dirabobi jiragen ruwan kai da su bi dokokin yadda ya kamata wajen daukar mutane, sannan su tabbatar da lafiyar jiragensu a ko wanne lokaci.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya dai, ta bayyana cewa suna ci gaba da yi wa iyalen wadanda lamarin ya shafa bayanai dangane da irin kokarin ceto wadanda abin ya rutsa da su.