'Yan IPOB 'yan ta'adda ne — Sojin Nigeria

Rundunar soji ta ce 'yan IPOB ba sa kaunar zaman lafiya

Asalin hoton, SIA KAMBOU

Bayanan hoto,

Rundunar soji ta ce 'yan IPOB ba sa kaunar zaman lafiya

Rundunar sojin Najeriya ta ayyana madugun kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra da magoya bayansa a matsayin 'yan ta'adda.

Wata sanarwa da daraktan watsa labarai na rundunar tsaron kasar Manjo Janar John Enenche ya aikewa manema labarai, ya ce kungiyar, "ta sauya zuwa barazanar tsaro ga kasar".

Ta kara da cewa, "Bayan mun yi nazari a tsanake kan abubuwan da ke faruwa a baya bayan nan, muna son sanar da jama'a cewa ikirarin da mambobin IPOB ke yi cewa ita ba kungiyar tayar da hankali ba ce ba gaskiya ba ne. Don haka abubuwan da suke yi ta'addanci ne".

Ayyana wannan kungiya a matsayi ta 'yan ta'adda na nufin za a iya kama su sannan a garkame su.

Sai dai matsalar da hakan za ta iya janyowa ita ce ta yadda rundunar sojin ta gaza gane irin goyon bayan da IPOB ke da shi a kudu maso gabashin kasar.

Haka kuma ayyana su a matsayin 'yan ta'adda ka iya haifar da wata matsalar.

Kazalika, sanya su a cikin jerin 'yan ta'adda na nufin dakarun sojin za su fuskanci kungiyoyin 'yan ta'adda uku wadanda suka hada da Boko Haram da tsagerun yankin Naija Delta da kuma su, ko da yake har yanzu rundunar ba ta iya murkushe ko wacce daga cikinsu ba.

Rahotanni na baya bayan nan na cewa madugun kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu da iyayensa sun bata.

Hakan na faruwa ne bayan sojoji sun kai samame gidansa a kauyen Afaraukwu da ke jihar Abia da ke kudu maso gabashin kasar ranar Alhamis da maraice.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Nnamdi Kanu ya ce dole a raba Najeriya

Wani dan uwan Kanu mai suna Prince Emmanuel Kanu ya shaida wa BBC ta wayar tarho cewa dakarun tsaron hadin gwiwa da suka hada da 'yan sanda da sojoji sun mamaye gidan mahaifin Kanu inda suka rika yin harbe-harbe.

Sai dai sojojin Najeriya sun ce ba ya gidan lokacin da suka je.

Ana ci gaba da zaman zullumi a yankin Kudu maso gabashiin Najeriya, inda aka samu wata hatsaniya tsakanin yan kungiyar neman kafa kasar Biafra ta IPOB da kuma sojin Najeriya da ke gudanar da wani atisaye a yankin, abin da ya haddasa asarar rayuka da dukiya.