Me Shugaba Buhari zai je yi a Amurka?

Shugaba Buhari zai hadu da sauran shugabannin duniya a wajen taron da shugaban MDD Antonio Guterres, zai karbi bakuncinsa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari zai hadu da sauran shugabannin duniya a wajen taron da shugaban MDD Antonio Guterres, zai karbi bakuncinsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai je birnin New York na Amurka a ranar Lahadi, domin halartar taron kwamitin koli na Majalisar DInkin Duniya, MDD, karo na 72, tare da sauran shugabannin kasashen duniya.

Abu mafi muhimmanci a ziyarsa tasa shi ne jawabin da zai gabatar yayin muhawarar, inda zai bayyana matsayar kasar.

A wata sanarwa da mai bashi shawara kan harkar yada labarai Femi Adesina ya fitar, ta ce babban dalilin halartar taron da shugaban zai yi shi ne gabatar da bayani a kan

Taken taron muhawarar na bana shi ne: 'Mayar da hankali kan mutane: Kokarin samun zaman lafiya da kuma Rayuwa mai kyau ga kowa da kuma duniya mai cike da nutsuwa.'

Shugaba Buhari zai hadu da sauran shugabannin duniya a wajen taron da shugaban MDD Antonio Guterres, zai karbi bakuncinsa.

Haka kuma, shugaban zai gana da Shugaba Trump a yayin cin abincin rana, tare da sauran takwarorinsa na sauran kasashen duniya.

Daga cikin manyan tarukan da Najeriya za ta halartar a yayin babban taron, har da wanda zai tattauna hanyoyin hana sa mata karuwanci da cin zarafinsu.

A lokacin taron, shugaba Buhari da 'yan tawagarsa zasu yi kokarin nuna Najeriya a matsayin wata mai kima, wadda ta san inda kanta ke mata ciwo, cikin jerin kasashen duniya.

Haka nan za a kara jaddada kokarin da Najeriyar ke yi wajen tabatar da dorewar zaman lafiya, da tsaro da kuma ci gaba a duniya, haka kuma idan bukatar hakan ta taso, a nemi karin hadin kan kasashen duniya a yaki da cin hnaci da rashawa

Sauran batutuwan da Najeriya za ta fi mayar da hankali kansu har da karfafa hukumomin kare hakkin dan adam da bin doka da kare 'yan gudun hijira sakamakon ayyukan ta'addanci da ambaliyar ruwa da kuma sauyin yanayi.

Cikin tawagar da za su yi wa shugaban rakiya har da gwamnonin jihohin Zamfara da Ebonyi da Ondo da kuma wasu manyan ministocinsa.

A kan hanyarsa ta dawowa, shugaban zai tsaya a Landan.