Bangladesh ta hana Msulimin Rohingya zuwa ko'ina

A Bangladeshi border guard stands guard at the Jalpatoli refugee camp for Rohingya Muslims near Gumdhum village in Ukhia, 16 September

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Jami'an tsaron Bangladesh na gadin sansanonin da 'yan kabilar Rohingyake zaune

Bangladesh ta sanar da cewa za ta dauki mataki mai girma da zai hana Musulmi 'yan kabilar Rohingya 400,000 wadanda suka tsallaka cikinta sakamakon kisan da ake yi musu a Myanmar tun watan Agusta zuwa ko'ina.

'Yan sandan kasar sun ce dole ne mutanen su ci gaba da zama a wuraren da gwamnati ta kebe musu kuma ba za su matsa ko'ina ba.

Bangladesh ta kuma ba da sanarwar gida matsugunai ga 'yan kabilar ta Rohingya 400,000 people a kusa da birnin Cox's Bazar.

Mutanen suna ci gaba da guje wa kisan da gwamnatin Myanmar ke yi musu, matakin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin kisan kare-dangi.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun bayyana cewa dakarun gwamnatin Myanmar sun kona kauyukan 'yan kabilar ta Rohingya.

Sai dai rundunar sojin kasar ta ce tana yunkuri ne na murkushe masu tayar da kayar baya amma ba farar hula ba.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da sabuwar takaddamar diflomasiyya ta barke tsakanin Bangladesh da Myanmar saboda kutsen da aka yi a sararin samaniyar Bangladeshi a makon jiya.

A wata sanar da rundunar 'yan sanda Bangladesh ta fitar ta ce ba za a bar Musulmi 'yan kabilar Rohingya su je ko'ina ba idan ban da wurin da gwamnati ta tanadar musu ba, ko da kuwa za su je wurin dangi ko abokansu ne.

An bukaci kamfanonin zurga-zurga da kada su dauki 'yan kabilar ta Rohingya domin kai su wani wuri, yayin da aka hana masu gidaje ba su haya.

Masu sharhi sun ce gwamnati ta dauki matakin ne domin hana 'yan kabilar ta Rohingya sajewa da jama'a.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Yawancin 'yan Rohingya na zaune ne a sansanoni