Jami'an tsaro sun kashe 'yan gudun hijira 30 a Congo

Congo Security

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Jami'an tsaro a gabashin Congo

Jami'an tsaro a gabashin Jamhoriyar Dimukradiyar Congo sun harbe 'yan gudun hijiran Burundi fiye da talatin har lahira.

Wakilin BBC a lardin Kivu ta Kudu ya ce wasu 'yan gudun hijirar da dama sun jikkata, sannan kuma an kashe wani dan sanda guda.

Jami'ai a kasar sun ce 'yan kasar ta Burundi goma sha takwas ne aka kashe.

Rahotanni sun ce jami'an tsaron Congo din sun bude wa 'yan gudun hijirar wuta ne bayan sun danna cikin wani kurkuku inda ake tsare da wasu 'yan kasar Burundi su hudu.

Dubban daruduwan 'yan kasar Burundi ne suka gudu daga kasarsu lokacin da tashin hankali ya barke a 2015, bayan shugaba Pierre Nkurunziza ya yanke shawarar neman shugabancin kasar a wa'adi na uku.