Hotunan bikin lasar gishiri na Jamhuriyar Nijar
Wasu hotunan bikin lasar gishiri da ake yi shekara-shekara a Jamhuriyar Nijar.

Ana yin bikin lasar gishiri shekara-shekara
Mahaya rakuma na baje-kolinsu
Mawaka da makada na cikin masu barje guminsu a wurin
Ana bai wa dabbobi mai gishiri domin inganta lafiyarsu
Jami'an tsaro na cikin shirin ko-ta-kwana
Mahalarta bikin na kashe kwarkwatar idanunsu
Mata da maza na halartar bikin
'Yan Jamhuriyar Nijar na alfahari da wannan biki
Bikin ya zama wata hanya ta nuna al'adun gargajiya
Shugabanni sun yi kira ga makiyaya su ci gaba da kula da dabbobinsu