'Buhari bai san halascin dimokradiyya ba'

Bayanan sauti

Ku saurari tattaunawa da Dr Junaidu Muhammad

Wani dattijon arewacin Najeriya Dr Junaidu Muhammadu ya shaida wa BBC cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai san halascin dimokradiyya ba shi ya sa 'yan kungiyar IPOB ba za su daina fafutikar neman raba kasar ba.

Dr Junaidu Muhammad shi ne jami`in da ya lura da kadarorin da `yan kabilar Igbo suka gudu suka bari a lokacin yakin basasar Najeriya.

Ya zargi gwamnatin Shugaba Buhari da sakaci wajen neman shawarwari daga mutanen da suka dace, har kungiyar IPOB ta Nnamdi Kanu na neman zama alakakai.

"Kowacce matsala akwai bukatar a samu mutanen da suka san abin da suke yi a sa su a gaba su ba da shawara. Wadansu ma ko ba su ba da shawara ba a je a nema su. Iko na Allah (SWT) ya sa watakila a samu waraka.

Amma daga ran da mutum ya dauka shi a idonsa babu wanda ya iya domin shi me mulki, to an shiga halaka mummuna. Rigimar da ake yi da wadannan mutane na IPOB da MASSOB ba sabuwar magana ba ce. Wadannan mutane suna gani sai sun mamaye kasar nan za a zauna lafiya. Idan ba su mamaye musamman arewa ba ba za a zauna lafiya ba domin raini ya shiga tsakani.

Ya kara da cewa masu fafutikar kafa kasar Biafra sun fahimci cewa za zu iya yin amfani da kasashen waje da kuma farfaganda "su yi mana lahani domin wadanda ke tafiyar da mulki ba su san abin da suke yi ba".

"Na farko dai idan za ka tattauna da mutane sai sun sani cewa ga wasu abubuwa da ka rike idan tattaunawar ba ta cimma gaci ba. Amma daga ran da mutum ya san za ka je ka tattauna da shi wa'azi za ka yi masa...ba za a zauna lafiya ba. Abin da ['yan IPOB] suka fahimta shi ne shugabancin kasar nan na yanzu ba shi da karfin zuciyar rike kasar, bai kuma san halascin dimokradiyya ba... shi ya sa idan za ka je tattaunawa irin wannan sai an yi dambe, an san karfin kowa sannan a zauna lafiya".

'Mun yi kokari kan Nnamdi Kanu'

Dr Junaidu ya ce bai gamsu da shugabancin Shugaba Buhari ba saboda shugaban ya kasa daukar kwararan matakai na gina gwamnatinsa.

"Misali, yau shekara biyu da watanni da kafa mulkin Buhari amma ba a nada jakadu ba sai kwanan nan. Yaya za ka nada jakada amma ka ce ba ka da abin da za ka tura shi ya je ya yi aikinsa bayan kuma rashin jakadan ya sa ana yi maka lahani".

Sai dai ministan harkokin wasannin Najeriya Mr Solomon Dalung ya shaida wa BBC cewa gwamnati ta dauki dukkan matakan da suka dace wajen dakile rikicin 'yan IPOB.

Bayanan sauti

Ku saurari hira da Mr Solomon Dalung

A cewarsa, "Ba mu kyale shi [Kanu] ba, mun kama shi kuma an kulle shi da dadewa yana hannun hukuma ana kai shi gaban alkali. Lokacin da yake tsare an samu sauki, amma da aka bayar da belinsa ne wadannan abubuwan ke faruwa".

Mr Dalung ya ce gwamnati za ta hukunta duk mutumin da ke da hannu a rikicin da 'yan kungiyar IPOB ke haddasawa komai daren dadewa.