Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi Amurka

Shugaba Buhari zai hadu da sauran shugabannin duniya a wajen taron da shugaban MDD Antonio Guterres, zai karbi bakuncinsa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari zai hadu da sauran shugabannin duniya a wajen taron da shugaban MDD Antonio Guterres, zai karbi bakuncinsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi birnin New York na Amurka domin halartar taron kwamitin koli na Majalisar DInkin Duniya, MDD, karo na 72, tare da sauran shugabannin kasashen duniya.

Shugaba Buhari ya tashi ne ranar Lahadi da safe.

Wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkar yada labarai Femi Adesina ya fitar ranar Juma'a, ta ce babban dalilin halartar taron da shugaban zai yi shi ne gabatar da bayani a kan halin da kasarsa ke ciki.

Taken taron muhawarar na bana shi ne: 'Mayar da hankali kan mutane: Kokarin samun zaman lafiya da kuma Rayuwa mai kyau ga kowa da kuma duniya mai cike da nutsuwa.'

Shugaba Buhari zai hadu da sauran shugabannin duniya a wajen taron da shugaban MDD Antonio Guterres, zai karbi bakuncinsa.

Haka kuma, shugaban zai gana da Shugaba Trump a yayin cin abincin rana, tare da sauran takwarorinsa na sauran kasashen duniya.

Daga cikin manyan tarukan da Najeriya za ta halartar a yayin babban taron, har da wanda zai tattauna hanyoyin hana sa mata karuwanci da cin zarafinsu.

Zai biya ta London

Mr Adesina ya ce Shugaba Buhari zai je London bayan ya kammala taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a Amurka.

Sai dai bai yi karin bayani kan abin da zai sa Shugaba Buhari zuwa London ba.

Kuma da BBC ta tuntube shi a kan batun, ya ce shugaban kasar zai ya da zango ne kawai a London, yana mai cewa ba zai ce komai ba bayan hakan.

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari ya gana da wasu gwamnoni gabanin tafiyarsa Amurka

A watan jiya ne shugaban na Najeriya ya koma kasar daga London bayan ya kwashe kwana 103 yana jinyar cutar da ba a bayyana ba.