Zanga-zanga ta barke kan shugabar da ba a zaba ba

President-elect Halimah Yacob (C) takes the oath of office while flanked by Singapore Prime Minister Lee Hsien Loong (L) and Chief Justice Sundaresh Menon (R) during the presidential inauguration ceremony at the Istana Presidential Palace in Singapore

Asalin hoton, Getty Images

Daruruwan mutane sun fantsama kan tituna don gudanar da wata zanga-zangar da ba a saba gani ba a Singapore.

Mutane na gudanar da wannan maci ne don nuna bijirewarsu ga zaben shugaban kasar wanda ba a yi takara ba a ranar Laraba.

An ayyana Shugaba Halimah Yacob a matsayin mace ta farko da za ta rike mulki Singapore.

Yayin zanga-zangar tsuke bakin an rika daga kyallaye da ke bayyana damuwa kan halin da dimokradiyya ta tsinci kanta a wannan kasa.

Ko da yake, ita shugabar nadi ce maimako wadda al'umma ta zaba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wani mutum na nuna rashin gamsuwarsa da yadda shugaba Halimah Yacob ta dare ga karagar mulkin kasar Singapore.

Halima Yacob ta kasance 'yar takara maras abokin hamayya bayan an soke cancantar wasu.

Rashin cika ka'idar tsauraran dokokin shiga zabe na kasar, ya sa aka haramta wa 'yan takara hudu tsayawa a zaben.