An kirkiro manhajar komfutar Hausa da ba irinta a duniya

Manhajar Rumbin Ilimi ta kunshi fannonin rayuwa daban-daban cikin harshen Hausa zalla

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manhajar Rumbun Ilimi ta kunshi fannonin rayuwa da fagen ilimi daban-daban a harshen Hausa zalla

A Najeriya, an kaddamar da wata manhaja mai suna Rumbun Ilimi, wadda ke kunshe da bayanai a kan fannonin rayuwa da fagen ilimi daban-daban cikin harshen Hausa zalla.

An kwashe shekara tara ana tsara manhajar kamar yadda wanda ya kirkiro ta ya bayyana a lokacin kaddamamarwar.

Mallam Abubakar Muhammad Tsangarwa, shi ne ya kirkiro manhajar, kuma ya shaida wa BBC cewa, manhajar ta kunshi darussa a bangarori na rayuwa daban-daban a cikin harshen Hausa.

Ya ce, ba sha'awa ba ce kawai ta sanya shi kirkirar manhajar, sai dai domin ya zaburantar da jama'a musamman masana kan su tashi su rika hidimta wa harshen.

Mallam Abubakar, ya ce, sai da ya laluba ya ga kwata-kwata babu wani abu da ya kunshi zallar Hausa na komfuta a duniya da ke bayar da gudunmawa a bangaren ilimi, sannan ya yi tunanin samar da manhajar.

Ya ce, an yi manhajar ne kuma don ta zamo mai amfani ga duk mutumin da zai iya karanta Hausa, walau ya je makaranta ko bai je ba.

Kazalika a manhajar, akwai magana a kan abinci mai gina jiki, da magana a kan ilimin zamantakewar dan-adam da Hausa da dai sauran fannoni da rayuwa da ilimi.

Malamin ya ce a yanzu akwai lambar da ake kira idan ana so a samu manhajar, wadda ita ce 08039648244, ga duk wanda yake bukata, ko da yake ya ce a yanzu suna kokarin yin 'yan gyararraki a kai, kafin nan da 'yan kwanki masu zuwa su kammala..

Sannan ya ce, an kirkiri shafin manhajar na intanet, wato www.rumbunilimi.com ko kuma a shafukan sada zumunta da muhawara na Facebook da Twitter a Rumbin Ilimi, sannan ta Whatsapp kuma a lambar da ya fada a baya, duk za a iya samun manhajar .