BBC ta kara bude wasu sabbin sassa a Ethiopia da Eritrea

Wani ma'aikatacin BBC na kallon sabon shafin Internet da aka bude
Bayanan hoto,

Sabbin rassan sun fara da farin jini

Kafar yada labarai ta BBC ta sake bude karin sassa guda uku amma na Internet, a kasashen Habasha, da makobciyarta Eritrea, a wani mataki na sake fadada yada shirye-shiryen da ba a taba gani ba tun shekarar 1940.

Rassan dai za su dinga kawo labaran ainahin abin da ke faruwa a yankunan da aka bude, a wani mataki na inganta yada labarai da BBC ke yi kamar yadda Editan BBC Willl Ross ya bayyana.

Nan da watanni masu zuwa za a sake bude rassan Amharic, da Afaan Oromo da kuma Tigrinya wanda za a bude hade da kafar yada labarai ta Rediyo.

A shekarar 2015 ne gwamnatin Birtaniya ta sanar da ware wasu kudade don sake inganta ayyukan da BBC ke yi a duniya. Wanda hakan ya sanya aka samu karin harasan da ya kamata a bude a Afirka da kuma yankin Asiya.

Shugaban sabbin rassan Will Ross, ya ce makasudin bude karin rassan shi ne saboda akwai mutane da dama da ke nuna damuwa kan rashin isassun labarai daga kasar Habasha da makobciyarta Eritrea, sai kuma harasan Amharic da Afaan Oromo da Tigrinya da akan yi korafin rashin gabatar da shirye-shirye ga wadanda suke jin harshen.

Kasar Eritrea dai ta samu 'yancin kai daga kasar Habasha a shekarar 1993, bayan shafe shekara 30 ana yaki.

An ci gaba da zaman doya da manja tsakanin kasashen biyu musamman ta iyakokinsu.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

An kuma yi kiyasin a kalla mutum 80,000 ne suka mutu tsakanin shekarar 1998-2000 a lokacin da kasashen suka yi yaki kan mallakar iyakokinsu.

Mista Ross, ya ce ya yi amanna gabatar da shiri da harasan kasashen biyu ci gaba ne ga BBC, ya kara da cewa kasashen na da yawan al'umma sama da miliyan 100, kuma shafukan sada zumunta za su yi matukar armashi ga matasan kasashen.

''Labaran da ake yadawa musamman a kasar Habasha ba sa wuce na siyasa, ko na sukar gwamnati da makamantansu. Wanda ba su kadai matasa suke son ji ba suna bukatar nishadi da labaran da za su dauke su can wata duniya ba wadda suka saba ba'', in ji Will Ross.

Tuni shafukan sada zumunta na Facebook da aka bude kan harasan uku suka yi matukar farin jini ba ga matasa kadai ba. Mutum 30,000 sun fara bibiyar shafin harshen Afaan Omoro cikin kwanaka uku kacal.

Sai dai akwai matsalar rashin karfin intanet a kasashen, don haka shirin bude sassan rediyo zai zama wani babban abu da BBC za ta yi ga 'yan Habasha da Eritrea.

Harasan Afirka:

 • Afaan Oromo: Yaren babbar kabilar kasar Habasha
 • Amharic: Yaren da ake amfani da shi a kasar Habasha a hukumance
 • Tigrinya: Babban yaren da ake aiki da shi a kasar Eritrea, tare da Larabci. Ana kuma amfani da shi a Habasha ma
 • Igbo: Yaren kabilar Igbo da ke Kudu Maso Gabashin Najeriya da kuma wani bangare na kasar Equatorial Guinea
 • Yoruba: Shi ne yaren da ake yi a yankin Kudu maso Yammacin NAjeriya da wasu sassan Afrika ta Yamma kamar Benin da Togo
 • Pidgin: Turancin Buroka wanda aka fi yin sa Kudancin Najeriya da Ghana da Kamaru da Equatorial Guinea

Harasan yankin Asiya:

 • Gujarati: Wani yaren da ake yi a jihar Gujarat da ke Indiya d
 • Marathi: Wani yaren da ake yi a jihar Maharashtra ta Indiya, ana kuma yi a birnin Mumbai na kasar
 • Telugu: Yaren da ke da dumbin masu yi kamar sauran yarukan Indiya, amma an fi yin sa a Andhra Pradesh da Telangana
 • Punjabi: Daya daga cikin yarukan da aka fi yi a duniya, akwai dumbin masu yin sa a Pakistan da wasu sassan Indiya
 • Korean: An yin sa a Arewaci da Kudancin Koriya, sai dai karin ya dan bambanta