Dan Nigeria ya lashe lambar yabo ta MDD kan taimakon 'yan gudun hijira

Zannah Mustapha with a pupil

Asalin hoton, Rahima Gambo/UNHCR

Malamin da ya dauki nauyin marayun yaran da mayakan Boko Haram da sojojin Najeriya suka kashe iyayensu ne ya lashe lambar yabo ta Hukumar Kula da 'Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a bana.

Da yake magana game da dalibansa, Zanna Mustapha ya ce, "Su ne suka fi kusanci da ni, kuma hakan zai iya zama sanadiyyar zaman lafiya a duniya baki daya."

Malam Mustapha shi ne wanda ya samar da daya daga cikin makarantun firamare kalilan da suka rage a birnin Maiduguri, inda ake fuskantar tashin hankali a Najeriya.

Haka kuma ya taimaka wajen sako 'yan matan chibok 82 da Boko Haram suka sace.

Malam Mustapha tsohon lauya ne, wanda kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen shiga tsakanin gwamnatin Najeriya da 'yan Boko Haram a kan sakin 'yan matan Chibok din da kungiyar ta sace a shekarar 2014.

Har yanzu sama da 'yan mata 100 ne daga cikin 276 da aka sace a shekarar 2014 ke hannun kungiyar ta Boko Haram.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A makon da ya gabata ne sama da 'yan matan chibok 100 da Boko Haram ta sako ne suka koma wurin iyayensu , kuma kwanan nan za su koma makaranta.

A wata makarantar addinin Musulunci mai suna Future Prowess, malaman da suke koyarwar suna karantar da daliban kyauta, su ba su abinci da kayan makaranta da magani duka kyauta.

Majalisar Dinkin Duniya ta karrama wadanda suka sadaukar da kansu wajen taimakawa 'yan gudun hijira.

Daga cikin wadanda aka karrama na baya-bayan nan sun hada da Graça Machel, da Luciano Pavarotti da kuma Eleanor Roosevelt.

"Ilimi na daya daga cikin manyan abubuwa da za su taimaka wa yara 'yan gudun hijira da rikicin tashin hankali ya rutsa da su ya kuma tilasta musu rabuwa da mahallansu," in ji babban kwamishinan kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya Filippo Grandi.

Ya kuma kara da cewa," Aikin da Malam Mustapha yake yi da tawagarsa na cikin abubuwa masu matukar muhimmanci".

A ranar biyu ga watan Oktoba ne ake sa ran za a gabatar da Malam Mustapha da lambar yabonsa a bikin da za a yi a Geneva na kasar Switzerland.