Bai dace a ayyana IPOB kungiyar 'yan ta'adda ba — Saraki

IPOB

Asalin hoton, STEFAN HEUNIS

Bayanan hoto,

A makon jiya ne dai rundunar sojin Najeriya ta ayyana IPOB a matsayin kungiyar ta'adda

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya ce ayyana kungiyar IPOB mai fafatukar kafa kasar Biafra a matsayin kungiyar 'yan ta'adda da sojin Najeriya ta yi, bai dace da kundin tsarin mulkin kasar ba.

A wata sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Bukola Saraki ya ce dokokin Najeriya sun fitar da matakan da za a dauka kafin a ayyana wata kungiya a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

A makon da ya gabata ne dai rundunar sojin Najeriya ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Bukola Saraki ya ce yana fatan cewar Shugaba Muhammadu Buhari, zai fara bin hanyar da ta dace wajen ayyana kungiyar a matsayin kungiyar 'yan ta'adda domin nuna wa duniya cewar Najeriya kasa ce wadda ke bin doka a ko wanne hali.

Saboda haka, Saraki ya ce wadanda suke ta magana a kan wannan su sha kuruminsu.

Kazalika, Sanata Saraki ya ce dole a jinjina wa rundunar sojin Najeriya kan kokarinta na wanzar da zaman lafiya a sassan kasar da kuma kiyaye hadin kan kasa.

Duk da haka, shugaban majalisar dattawan ya ce ya kamata sojin kasar su bi horarwar da suka samu na mutunta hakkin bil'adama a lokacin da ake takalar su.

Asalin hoton, .

Bayanan hoto,

Kadan daga cikin sanarwar da Bukola Saraki ya wallafa a shafinsa na Twitter