Kotu ta bayar da umarnin kai 'yan IPOB 67 kurkuku

Nnamdi Kanu

Asalin hoton, STEFAN HEUNIS

Bayanan hoto,

Har yanzu ba a san inda shugaban IPOB yake ba

Wata babbar kotun Najeriya da ke kudu maso gabashin kasar ta bayar da umarnin kai a kalla mutum 67 'yan kungiyar IPOB gidan yari, kan zarginsu da hannu a tashin hankali na fafatukar kafa kasar Biafra.

Sojoji sun kama yawancin mutanen da ake zargi da kasancewa 'yan kungiyar IPOB ne kusa da Isiala Ngwa, yayin da 'yan sanda suka kama mutum bakwai da zargin kona ofishin 'yan sanda na Ariara da ke Aba, wata cibiyar kasuwanci a kudu maso yammacin kasar.

Mutanen sun musanta zargin da ake yi musu.

Sojin Najeriya dai ta ayyana kungiyar IPOB mai fafatukar neman kafa kasar Biafra a matsayin kungiyar 'yan ta'adda bayan sojoji sun yi arangama da magoya bayan kungiyar kusa da gidan shugaban kungiyar, Nnamdi Kanu da ke jihar Abia.

Arangamar ta sa mutane sun ji raunuka kuma ana zaman dar-dar.

A baya-bayan nan dai ana samun karuwar tashin hankali a kudu maso gabashin kasar daga kungiyar IPOb a fafutukarsu ta neman kafa jamhuriyyar Biafra.