'Yan Ghana sun yi zanga-zanga kan musgunawa Musulman Rohingya

Rohingya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Majalisar Dinkin Duniya ta koka da yadda ake musguna wa Musulmi 'yan kabilar Rohingya a Myanmar

Wasu daruruwan Musulmai a birnin Accra na kasar Ghana sun gudanar da wata kasaitaciyar zanga-zanga don nuna rashin jin dadinsu da cin zarafin da suka ce ake yi wa Musulmai 'yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.

Masu zanga-zangar sun kuma nuna rashin jin dadinsu game da abun da suka kira ci gaba da sayar wa kasar makamai da kasar Israila take ci gaba da yi.

Sai dai, a dai dai lokacin da masu zanga zangar suke shirin shiga gari, sai 'yan sanda suka dakatar da su.

Ga karin bayanin da abokin aikinmu Iddi Ali ya aiko mana, sai ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraro:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Rahoton Iddi Ali kan zanga-zangar Myanmar

Labarai masu alaka