An haramta wa Rooney tuka mota shekara biyu

An haramta wa Rooney tuka mota na tsawon shekara biyu
Tsohon kyaftin din Ingila Wayne Rooney ya gurfana a gaban kuliya inda ake tuhumarsa da yin tuki cikin maye.
An kama shi ne a lokacin da 'yan sanda suka tsayar da motarsa a Wilmslow, a safiyar 1 ga watan Satumba.
An haramta wa dan kwallon mai shekara 31 yin tukin mota na tsawon shekara biyu, an kuma umarce shi da yin aikin baban-giwa na sa'a 100 ba tare da an biya shi ba, a matsayin cikon umarnin da kotun ta ba shi na yi wa al'ummarsa hidima.
Haka kuma an umarce shi da biyan fam 170 a lokacin da ya gurfana a kotun majistare a Stockport.