Kun san wadanda suka yi ikirarin sune bayyanar Annabi Isa?
Kun san wadanda suka yi ikirarin sune bayyanar Annabi Isa?
A wani sabon littafinsa, The Last Testament, ko 'Alkawari na karshe', mai daukar hoto Jonas Bendiksen, ya tara labaran wasu mutane da suka yi amannar cewa sune bayyanar Annabi Isah ta karshe.
A cikin shakara biyu, ya yi yawo a cikin duniya don haduwa da mutane bakwai daban-daban da suka fito karara suka yi ikirarin cewa sune Al-Masihu da suka dawo duniya.
Ya shaida wa BBC game da aikin da ya yi don gano wadannan mutane da mabiyansu.