'Yadda na tsinci hannun kanwata a baraguzan gini'

'Yadda na tsinci hannun kanwata a baraguzan gini'

Wannan bidiyo ne a kan yadda wani mutum ke bayyana yadda ya tsinci hannun kanwarsa a cikin baraguzan gini, bayan bala'in zaftarewar kasa a Saliyo.

Wata daya da ya gabata ne Saliyo ta gamu da bala'in zaftarewar laka da ambaliyar ruwa a Freetown babban birnin kasar, inda aka kiyasta cewa mutum 1,300 sun mutu.

An binne daruruwan mutanen da suka mutu a zaftarewar lakar da ta afku a Tsaunin Sugar Loaf.

Thomas, wanda ya rasa mutum takwas daga iyalan gidansa, ya shaida wa BBC halin da ya shiga sakamakon wannan bala'i.