An kai harin bam wajen karbar agaji a Borno

Hari a Borno

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An sha kai hare-hare kan fararen hula a jihar Borno

Wasu rahotanni daga arewa maso gabacin Najeriya na cewar an kashe a kalla mutum 15 a lokacin da wasu 'yan kunar bakin wake biyu suka kai hari a wani wurin da fararen hula suke karbar agaji da safiyar ranar Litinin.

Rahotannin sun ambato wani ma'aikacin ceto da kuma 'yan sintirin farar hula da ake kira civilian JTF na bayyana cewar an kai harin ne a kauyen Mashamari da ke kusa da Konduga.

Wasu mutanen fiye da 40 ne dai aka ce sun samu rauni sakamakon tagwayen hare-haren.

Ana dai kyautata zaton cewar kungiyar Boko Haram ce ta kai harin, wadda ta kwashe shekaru tana kai hare-hare a yankin na arewa maso gabashin Najeriyar.

Ga karin bayanin da Abdulhamid Gazali, wani dan Jarida a Maiduguri, babban birnin jihar ta Borno, ya yi wa abokin aikinmu Aminu Abdulkadir:

Bayanan sauti

Karin bayanin da Abdulhamid Gazali kan harin Borno