Takunkumi zaburad da mu zai yi - Koriya ta Arewa

Shugaba Kim Jong-un da manyan hafsoshin sojinsa na murnar gwajin makami mai linzamin da suka yi ranar Juma'a

Asalin hoton, AFP Getty

Bayanan hoto,

Koriya ta Arewar ta ce takunkumin kara mata kaimi zai yi a shirinta na kera makaman kare dangi

Koriya ta Arewa ta yi gargadin cewa kara sanya mata takunkumi da kuma matsin lamba a kan shirinta na kera makaman kare dangi ba abin da za su yi , sai dai ma su kara sa ta tashi tsaye a shirin.

A wata sanarwa mai dauke da kausasan kalamai, Pyongyang, ta bayyana sabbin jerin takunkumin Majalisar dinkin duniyar da cewa su ne mafi cutarwa da suka saba ka'ida da kuma tsananin mugunta ga dan adam.

A yayin da Koriya ta Arewar ke wannan kalami, shugabannin Amurka da China sun kara jaddada aniyarsu ta tsananta matsin lamba a kan Koriyar ta hanyar kara tabbatar da sabbin takunkumin na Majalisar dinkin duniya.

Tun da farko Amurka da Koriya ta Kudu sun gudanar da atisayen soji na hadin guiwa.

A ranar Juma'a ne Koriya ta Arewa ta harba makaminta mai linzami na baya-bayan nan ya ratsa Japan.

Makamin ya yi tafiyar nisan kilomita 3,700, inda ya cimma yankin Amurka na tekun Pacific, Guan, yankin da Koriya ta Arewar ta ce tana son cimma da makamin.

Koriya ta Arewar ta yi wannan gwaji ne bayan sabbin takunkumin da Majalisar dinkin duniya ta sa mata, kuma 'yan kwamitin tsaro na majalisar dukkaninsu sun allawadai da shi da murya daya, tare da cewa tsokana ce kawai.

A sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewar ta fitar, ta kamfanin dillancin labaran kasar, ta ce karin matsin lambar da Amurka da 'yan kanzaginka ke yi na sanya mata takukumi da matsin lamba ba zai cimma buri ba, sai dai akasin haka domin hakan zai zaburad da ita ne wajen ganin ta kammala hada makamanta na nukiliya.

Sannan kuma ta ce takunkumin da aka amince da sanya mata ranar 11 ga watan Satumba, an yi shi ne da nufin kashe al'ummar kasar da tsarinta da kuma gwamnatinta.

Ta ce jerin takunkumin wani shiri ne na jefa Koriya ta Arewa cikin matsanancin rashin mai da kuma kudin gudanar da shirinta na makaman nukiliya, da takaita mata shigo da mai da kuma haramta mata fitar da kayan masakunta.

Sabon matakin sanya takunkumin ya biyo bayan gwaji na shida kuma mafi karfi na makamin nukiliya da Pyongyang ta yi a farkon watan nan.