Ba na tsoron a bincike ni kan Musulmin Rohingya – Suu Kyi

Myanmar's State Counsellor Aung San Suu Kyi speaks during a joint a press conference with Sweden's Prime minister at the Rosenbad government office on 12 June 2017 in Stockholm, Sweden.

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto,

Misis Suu Kyi tana shan suka game da rikicin Rohingya

Shugabar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi, ta ce gwamnatinta ba ta tsoron ''binciken kasa da kasa'' game da rikicin Rohingya.

Wannan ne jawabinta na farko ga al'ummar kasar tun bayan fara rikici a jihar Rakhine da ke arewacin kasar.

Rikicin ya sa Musulmi 'yan kabilar Rohingya fiye da 400,000 tserewa kasar Bangladesh, mai makwabtaka.

A jawabin da ta yi wa majalisar dokokin Myanmar da harshen Turanci, Aung San Suu Kyi ta ce ta damu matuka game da "dukkan mutanen" da rikicin ya shafa.

Ta kara da cewa Myanmar "ta dukufa wajen lalubo hanyar magance rikicin."

Ms Suu Kyi, wanda ta kauracewa babban taron Majalisar Dinkin Duniya wanda za a fara ranar Talata a birnin New York, ta ce tana son kasashen duniya su san matakan da gwamnatinta take dauka.

Sai dai sa'o'i bayan jawabinta, Hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a ba ta damar shiga yankin don ta "gane wa idonta" hakikanin halin da ake ciki a yankin.