Za a sake dage zaben kasar Kenya

Raila Odinga
Bayanan hoto,

Wannan hoto na nuna jagoran 'yan adawa Raila Odinga ya na kalubalantar zaben da aka yi a watan Agusta

Kamfanin da zai samar da na'urar zamani da za a sake gudanar da zabe da ita a kasar Kenya, ya ce kayan aikin ba za su samu ba kafin karshen watan gobe kamar yadda aka shirya da za a sake yin zaben shugaban kasa.

Kotun kolin kasar ce dai ta soke zaben da aka gudanar, bayan madugun 'yan adawa Raila Odinga ya yi zargin an tafka magudi a zaben da shugaba mai ci Uhuru Kenyatta ya yi nasara.

Kamfanin OT-Morpho mallakar kasar Faransa, ya ce yana bukatar a sake inganta na'urar zaben dan haka ba bu tabbas din ko za a yi zaben a ranar 17 ga watan gobe kamar yadda aka tsara ba.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya samu damar ganin kwafin wasu takardu da kamfanin OT-Morpho ya aikewa hukumar zaben kasar Kenya.

A ranar 18 ga watan Satumba aka aike da wasikar wadda ke nuna an yi amfani da na'urori iri biyu a lokacin zaben dan haka kowacce ta na bukatar ayi mata duba na tsanaki dan kaucewa yin kuskure.

Dan haka akwai ayyukan da ba lallai a kammala su akan lokaci ba. Haka kuma wani babban jami'i a hukumar zaben ya tabbatarwa da BBC batun dage zaben a karo na biyu.

An samar da kwamfiyuta na hannu sama da 45,000 a lokacin zaben, wadda akai amfani da ita dan tantance masu kada kuri'a, da daukar tambarin yatsun su da kuma daukar hoto kafin su kada kuri'a.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a watan Afrilu da ya wuce, ya ce na'urorin sun taka rawa wajen tafiyar da zaben cikin sauki.

Sai dai kotun koli ta ce daya daga cikin dalilan da suka sanya aka soke zaben shi ne rashin ingancin na'urar zabe, da kuma zargin tafka magudi da aringizon kuri'u.

Sai dai a ranar Alhamis mai zuwa ne ake sa ran kotu za ta sanar da matsayarta kan batun baki daya.

Baya ga matsalar na'ura, madugun 'yan adawa Raila Odinga da ya ke son ko ta wanne hali ya yi nasara a kan shugaba Uhuru Kenyatta ya ce ba zai taba amincewa a yi zaben ba matukar ba a sauya baki daya ma'aikatan hukumar zabe ba.

A bangare guda kuma a gobe Laraba ne hukumar zaben ta shirya wani zama na musamman da 'yan takarar biyu, don warware matsalolin gabannin zaben.