Snapchat ya toshe Al Jazeera a Saudiyya

'Yan Saudiyya na amfani da wayoyin zamani na komai da ruwan ka irinsu Iphone
Bayanan hoto,

Saudiyya ce ja gaba a kasashen gabas ta tsakiya da 'yan kasar ke amfani da kafafen sada zumunta na zamani

Kafar sadarwa ta Snapchat ta toshe kafar yada labarai ta Al Jazeera a kasar Saudiyya.

Snapchat ya dauki matakin ne bisa umarnin da hukumomin Saudiyya suka ba da na cire baki daya kafar yada labaran mallakar kasar Qatar, saboda kasar ta bijirewa umarnin kasashen Labarawa da ke yankin Gulf da hakan ya sabawa dokokin kasashen.

Qatar dai na takun saka da Saudiyya da wasu kasashen Larabawa da suka hada da Masar, da Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Kasashe hudun sun yanke duk wata alaka da Qatar ciki kuwa har da huldar kasuwanci da sauran su.

A farkon shekarar nan ne Saudiyya da kawayenta suka zargi Qatar da taimakawa kungiyoyin 'yan ta'adda, zargin da ta musanta.

Saudiyya dai ta kafawa kafar yada labarai ta Al Jazeera kahon zuka, cikin sharuddan 13 da kasashen suka kafawa Qatar har da rufe kafar yada labaran ta Al Jazeera kafin su warware takunkumin da suka kakaba mata, duk da daga baya sun janye.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce Saudiyya kasa ce da 'yan cikinta ba su da 'yancin fadar albarkacin bakinsu ko da kuwa ta kafafen sada zumunta na zamani ne.

Cikin kasashen gabas ta tsakiya Saudiyya ita ce ja gaba da matasan kasar ke amfani kafafen sada zumunta da muhawara, hakan bai rasa nasaba da yawan mutanen da ke amfani da wayoyin zamani na komai da ruwanka irinsu Iphone ba.

Mai magana da yawun kamfanin Snapchat ya ce kawo yanzu ba za su ce uffan kan batun ba, sai dai ya jaddada cewa Snapchat na kokarin ganin bai take dokar kasashen da yake hulda da su ba, don haka Saudiyya da ta bukaci a toshe kafar Al Jazeera ba su da zabin da ya wuce aikata hakan.