Za mu lalata Korea Ta Arewa idan tura ta kai bango - Trump

US President Donald Trump at the UN General Assembly in New York, 19 September

Asalin hoton, EPA

Shugaba Donald Trump ya shaida wa babban taron Majalisar Dinkin Duniya cewa Amurka za ta lalata Koriya Ta Arewa idan har tura ta kai bango don ta kare kanta da kawayenta.

A jawabinsa na farko a taron, ya yi wa Shugaba Kim Jong-un shagube da cewa: "Mamallakin makamin kare dangi zai yi kunar bakin wake."

Koriya ta Arewa ta harba makaman nukiliya da na kare-dangi duk da gargadin da Majalisar Dinkin Duniya ke mata.

Jim kadan kafin Mista Trump ya yi magana, Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya bukaci hadin kan kasashe, inda ya ce: "Ba zai yiwu mu yi likimo har yaki ya cim mana ba."

Shugaban na Amurka ya kuma soki Iran, inda yake cewa, "kasa ce da ta yi kaurin suna wajen mulkin kama karya da kuma cin hanci da rashawa," wadda ke da niyyar kawar da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya.

Ya yi kira ga gwamnatin Iran ta daina goyon bayan ta'addanci, ya kuma soki yarjejeniyar da aka yi lokacin mulkin Obama kan shirin nukiliya, wanda ya ce hakan abin kunya ne.

A sauran bangarorin jawabansa, ya ce:

  • Amurka ba za ta sake yarda ta shiga yarjejeniyar bangare guda ba
  • Ba za a yarda da, ko zura ido kan rikicin kasar Venezuela, wadda gwamnatin masu tsattsauran ra'ayin kawo sauyi (gurguzu) da ba sa ga maciji da Amurka ke jawowa ba
  • ya yi watsi da ra'ayin gurguzu yana mai cewa hakan bai jawo komai ba sai tashin hankali da rashin nasara.

Amurka ta sha gargadin Koriya Ta Arewa kan gwaje-gwajen makaman nukiliyarta, wanda hakan ya sabawa dokokin Kwamitin Tsaro na MDD.

A watan da ya gabata ne rikicin ya yi kamari lokacin da Koriya ta sanar da shirye-shiryen gwajin makamin nukiliyarta a yankin Pacific na Amurka da Guam.

Mista Trump ya ce, "Idan aka tilastawa Amurka ta kare kanta ko kawayenta, to ba mu da wani zabi sai na lalata Koriya."

Wani babban jami'i a wata cibiya ta bincike a New York kan harkokin kasashe waje Stewart Patrick, ya ce, barazanar Shugaba Trump na lalata Koriya 'abu ne da hankali ba zai dauka ba.'

Ya shaida wa BBC cewa: "Ban gamsu da wannan batu ba."

Asalin hoton, Getty Images