Sulhu ya dace da Koriya ta Arewa – Buhari

Asalin hoton, Getty Images
Bana ne karo na uku da shugaban yake halartar taron wanda ake yi kowace shekara a cikin watan Satumba
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci kasashen duniya da su sanya baki a kan takaddamar kasar Koriya ta Arewa da kasashen Yammancin Duniya.
Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 wanda ake yi a birnin New York na kasar Amurka ranar Talata.
Ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta samar da wani kwamiti don warware takaddamar makamin Nukiliyar Koriya ta Arewa.
Ya ce ya kamata kwamitin ya kunshi "wakilai daga ko wane bangare na duniya."
Sauran batutuwan da shugaban ya tabo a jawabinsa sun hada da yaki da cin hanci da dimokradiyya da kuma kyakkyawan shugabanci a nahiyar Afirka.
Bana ne karo na uku da shugaban yake halartar taron wanda ake yi kowace shekara a cikin watan Satumba, inda shugabannin kasashen duniya fiye da 100 ke halarta.