Ango da amarya sun roki baki su dauki nauyin bikinsu

Ango Ben da Amarya Clare
Bayanan hoto,

Ben da Clare sun shafe shekara 6 su na tare, kuma su na da 'Ya mai shekara 3

Wasu amarya da ango da ba su da kudin yin biki na kece reni, sun roki mahalarta bikin ko wanne ya ba su tallafin fan 150, kuma za su ba da kudin ne ta hanyar amfani da wata 'yar na'ura da angon ya samar da za ta tara kudin a ciki.

Ango Ben Farina ya ce ranar bikin aurensu da Clare Moran a watan Yuni zai zamo abin ban sha'awa da nishadantarwa ga wadanda suka halarci bikin.

Cikin abubuwan da mahalarta bikin auren za su biya har da kwanaki uku da za su yi a wurin da za a gudanar da shagalin na kece raini a Derbyshire, da ango Ben ya ce har da katon kwamin wanka, da wurin da za a yi musu gyaran jiki na zamani da ake kira Spa.

Wasu dai na cewa Mista Ben ya tsauwala kudin da ya bukata, amma ya dage cewa babu wata tsawwalawa da ya yi saboda dukkan wadanda za su halarci bikin aure sun amince da hakan.

Kawo yanzu dai dukkan mutane 60 da za su halarci bikin, da kuma 'yan yara 20 sun amince za su halarci bikin har ma sun ce za su ba da kafin alkalami kafin lokacin ya zo.

Bayanan hoto,

Za a yi auren masoyan ne a Knockerdown Cottages da ke Derbyshire

Mutane na biyan makudan kudade don su halarci bikin aure, maimakon su kashe kudin yayin da tafiyar mai zai hana ba za su bai wa ma'auratan da suke shirya bikin ba don su ma su samu karsashi ba, ina ganin ba abin damuwa ba ne,'' in ji wani mai shirya bikin aure Mista Farina, dan asalin Leicester.

"Na ba su wurin ne a matsayin na alfarma, saboda hatta abincin da za a ci lafiyayye ne har da kayan shaye-shaye masu dadin dandano, kuma duk a cikin kudinsu.''

''Sannan kamar yadda na yi bayani, akwai kwamin wanka katon gaske da za su shiga su yi ninkaya da motsa jiki, da kuma wuri na musamman da za a gyarawa 'yan biki jikinsu, tun daga fata har zuwa wanke gashi da kafa da sauransu,'' in ji ango Ben.

Mista Farina, ya ce shi da abokansa da suka halarci wani biki, sai da suka kashe fam 550, kuma bikin a kasar Girka aka yi shi, don haka da suka sun kara kashe fam 1,200 kuma baki daya kwana daya kacal suka yi.

Don haka ya ce bai kamata mutum ya kwana a otal din da ya fi fam 100 ba, idan har bikin aure ya zo, sannan idan ya shiga wurin sayar da kayan shaye-shaye bai kamata ya kashe sama da fam 50 ba.

Bayanan hoto,

Ango Ben ya ce wadanda suka halarci bikin auren su, zai fi kama da sun zo hutawa ne saboda ababen jin dadin da aka tara a wurin, irin wannan kwamin wanka