Jam'iyyar ƙin musulunci ta samu tagomashi a Jamus

German Proteters Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu zanga-zanga sun auka kan tituna don nuna adawarsu kan tagomashin da AfD ta samu

Zaben majalisar dokokin Jamus ya ba shugaba Angela Merkel damar zarcewa wa'adi na hudu a kan mulki.

Ko da yake, ya rage mata kason kuri'un da jam'iyyarta ta samu zuwa 33 cikin 100, adadi mafi karanci a shekaru gommai.

Mrs Merkel za ta shiga tattaunawa mai wahala don kafa gwamnatin gambiza a wani yanayin siyasa maras alkibla.

Ana sa ran tattaunawa ce da sai an kai ruwa rana.

Image caption Sakamakon zaben dai bai yi wa Angela Merkel dadi ba duk da nasarar da ta yi ta samun wa'adin mulki na hudu

Karon farko, bayan samun kasa da kashi 13 cikin 100, jam'iyyar AfD mai tsattsauran ra'ayin kishin kasa za ta karbi kujeru a majalisar Busdestag.

Wakilin BBC a Berlin ya ce jam'iyyar da ke gud'ar samun nasara yanzu, ita ce AfD mai janyo rarrubuwar kai, ta masu ƙin jinin baƙi da addinin musulunci.

"Kasa da shekara biyar bayan kafuwarta, mai yiwuwa a yanzu AfD ta tashi da kujera 100 a Majalisa," in ji shi.

Haka zalika, sakamakon ya janyo fushi da nuna taraddadi a kasar ta Jamus.

Zanga-zangar nuna adawa da jam'iyyar AfD ta barke a birane da dama ciki har da Berlin, an ma kama adadin mutane da dama.

Jazaman ne sai gwamnatin da Merkel za ta kafa ta samu hadin kan jam'iyyu ƙanana guda biyu bayan 'yan Social Democrat sun sanar cewa ba za su shiga gamin gambizar ba.

Hakan ya biyo bayan mummunan kayan da suka sha wanda rabonsu da ganin irinsa tun a shekarun 1930.

Rashin tabbas ya sa darajar takardar kudin euro tangal-tangal a kasuwannin Asiya bayan sanar da sakamakon zaben.

Labarai masu alaka