Buhari ne da kansa ya ɓata lamarin – Kungiyar Igbo

John Nwodo
Image caption Jagoran Ohaneze Ndigbo ya ce ba sa goyon bayan masu rajin ballewa daga Najeriya amma suna son a sake wa kasar fasali

Kungiyar Ohaneze Ndigbo a Najeriya ta zargi Shugaba Muhammadu Buhari da abin da ta kira "bata lamari" ta hanyar watsar da al'ummar Igbo a gwamnatinsa.

Yayin hira da BBC lokacin wata ziyara, shugaban kungiyar, Cif John Nwodo ya ce batun mayar da 'yan kabilar Igbo saniyar ware, ba boyayyen abu ba ne.

Hakan na faruwa ne, tun bayan jawabin da ya ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi cewa zai bambanta tsakanin 'yan kasar bisa la'akari da kuri'un zaben da suka ba shi.

A cewarsa: "Buhari ya fada wa duniya cewa zai bambanta kulawar da zai yi wa mutanen da suka kada masa kashi 97 cikin 100 na kuri'unsu da wadanda suka kada masa kashi biyar na kuri'unsu."

Jagoran Igbon ya ce ba a ba wa 'yan kabilarsa gwargwadon hakkokin da suka cancanci samu.

John Nwodo ya buga misali da gwamnatin jamhuriyar ta biyu. Inda ya ce kuri'ar da Shagari ya samu a yankin Kudu Maso Gabas ba ta kai wadda ya samu a yankin Middle belt ba, kuma ba ta sa shi nuna wa Igbo bambanci ba.

"Ka ga! Ni tsohon dan jam'iyyar NPN ne, na rike mukamin minista a gwamnatin Shagari, in ji shi."

Ya ce bai kamata Buhari ya yi fatali da 'yan kabilar Igbo, don kawai ba su kada masa kuri'a ba.

A cewarsa, shugaban kasa baban kowa ne, don haka bai dace ya kori 'ya'yansa don kawai sun bijire masa ba.

Ka duba hukumomin tsaro a Najeriya, babu ko da daya da dan kabilar Igbo ke jagoranta.

"Mu, ba ga babban hafsan tsaro ba, mu ba ga babban hafsan sojin kasa ko na ruwa ko sojin sama ba. Ba a ba mu shugabancin hukumar kula da shige da fice ba, ko ta leken asiri ko ta tsaron farin kaya ko ta kiyaye hadurra ba."

"Ba mu da komai. Wannan ta sa aka mayar da mu tamkar al'ummar da aka ci ta da yaki," a cewarsa.

Ya yi ikirarin cewa an girke musu shingayen 'yan sanda a duk manyan hanyoyin yankin Kudu Maso Gabas babu gaira babu dalili.

John Nwodo ya ce kusan illahirin kwamishinonin 'yan sandan jihohin yankin Igbo, sun fito ne daga arewacin Najeriya.

"Babban kwamandan da ke kula da runduna ta 82 da ke Enugu, dan arewa ne. Shin sun san yankin ne?" Nwodo ya tambaya.

Cif John Nwodo ya ce yana alla-alla ya samu ganawa da Buhari don zayyana masa wadannan batutuwa da ke ci wa kabilar Igbo tuwo a kwarya.

Labarai masu alaka