Nigeria: Zaki ya kashe mai kula da shi a Ibadan

Zaki Hakkin mallakar hoto Getty Images

Hukumomi a Najeriya sun rufe wani gidan namun daji (Zoo) bayan wani zaki ya kashe wani ma'aikacin gidan.

Al'amarin ya faru ne a gidan Zoo na Agodi a makon jiya a jihar Oyo da ke kudu-maso-yammacin kasar, kamar yadda gwamnatin jihar ta tabbattar.

Magarigayin mai suna Hamzat Oyekunle ya mutu ne sanadiyyar raunin da ya ji yayin da zakin ya kai masa hari.

Rahotanni sun ce marigayin ya kwashe "tsawon shekara biyar yana ciyar da zakin kuma ya saba da dukkannin dabbobin da ke gidan Zoon."

Gwamnatin jihar wadda ta bayyana rashin jin dadinta kan al'amarin ta ce an fitar da zakin daga gidan Zoon yayin da ake ci gaba da bincike.

Karanta wasu labaran masu kayatarwa

Labarai masu alaka