Mata 100: Shin mata masu mulki na taimakon sauran mata?

Hillary Clinton supporters at the Javits Center Hakkin mallakar hoto KENA BETANCUR
Image caption Ana ganin cibiyar Javits tana da rufin gilashi mafi girma a New York, kuma ta gama shiryawa tsaf don zama shugabar kasar Amurka mace ta farko a tarihi

"Na kasa yarda da cewa mata sun kai matakin da ba su taba kai wa ba zuwa wannan lokaci, idan akwai wasu 'yan matan da ba su yi bacci ba don kallon wannan abin da ke faruwa - to ina son shaida muku cewa akwai yiwuwar in zama mace shugabar kasar Amurka ta gaba, sannan daya daga cikinku ka iya biyo baya."

Wadannan su ne kalaman da Hilary Clinton ta taba yi a lokacin da ta samu nasarar zama 'yar takarar jam'iyyar Democrat a shekarar 2016.

A karshe ta gaza kai wa ga samun nasara, sai dai zabar wajen da ta gudanar da taron nata a wannan dare ba komai ba ne face akasi.

Ana ganin cibiyar Javits tana da rufin gilashi mafi girma a New York, kuma ta gama shiryawa tsaf don zama shugabar kasar Amurka mace ta farko a tarihi.

Wato an zaci ko za ta iya ragargaza rufin gilashin nan kamar yadda yake a karin magana ta Turanci, 'Women breaking the glass ceiling,' wato mata masu kai wa wani matsayi da ba a saba gani ba.

Sai dai Mrs Clinton ba ta kai gaci ba - amma yawan matan da ake zabar su don yin mulki ya rubanya sau biyu a duniya cikin shekara 10 da suka gabata.

A cewar wani bincike da cibiyar Pew , yanzu haka akwai mata 15 da suke rike da mukamai, takwas daga cikinsu su ne shugabanni mata na farko a kasarsu.

Amma duk da haka har yanzu shugabanni mata na kadan ake da su a duniya inda ake da kashi 10% kacal kasashe 193 da suke mambobin ne Majalisar Dinkin Duniya.

Hakkin mallakar hoto DIPTENDU DUTTA
Image caption Kungiyar matan Indiya a kan hanyarsu ta zuwa West Bengal

A zahiri wadannan matan suka yi nasarar kai wa gaci, amma abin tambaya a nan shi ne, ko suna inganta rayuwar sauran matan da suke kasarsu?

Tsarin mulki a kananan hukumomin Indiya za su iya bayar da wannan amsar.

Tun shekarar 1993, an bukaci daya daga cikin kauyuka uku na Indiya da su kebe mukamin babbar kansila ga mace, don kirkiro da wani yanayin rayuwa.

Wani bincike da aka yi a Indiya a shekarar 2012 ya gano cewa, samun shugaba mace na kara shakuwa da dangantaka ta kut-da kut ga mata matasa a kauye.

Da aka tambayesu abin da suke bukata game da 'ya'yansu ta fuskar ilimi, yayin da suka samu dansu na farko da kuma aikin yi, sai aka ga cewa dukkan iyaye na da tsananin buri a kan 'ya'yansu maza.

Amma duk lokacin da aka samu mace shugaba a kauye a karo biyu, iyaye za su rage buri, za a samu raguwar bambanci da iyaye ke nunawa tsakanin yara maza da mata da kusan kashi 20% idan aka kwatanta da wadanda ba su taba samun shugaba mace ba.

Marubutan sun gano cewa shugabanni mata ba sa fuskantar kalubale wajen sauya yanayin mata da 'yan mata ta hanyar tsare-tsarensu.

Sai dai samunsu a matsayin masu taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba ya isa ya kara ilmantar da zabuwar da matan da suke kusa da su.

Hakkin mallakar hoto Sean Gallup
Image caption Hillary Clinton da Angela Merkel

Har ila yau binciken da aka yi na 2012 ya nuna cewa shugabanni mata na jan hankali a yanayin jagoranci, ko da kuwa daga nesa ne.

Wadanda suka rubuta rahoton sun gayyaci dalibai mata suka raba su zuwa gida hudu don gabatar da jawabi a gaban wani yanayi mai kama da zahiri, bangare daya sun ga hoton shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, daya kuma sun ga hoton Hillary Clinton (Sakatariyar harkokin Amurka), daya sun ga Bill Clinton daya bangaren kuma da suka fi karfi ba su ga hoto ko daya ba.

Majalisar tattalin arziki ta duniya (WEF) ta bai wa wasu kasashe lambar yabo a wani rahotonta na Samun daidaiton Jinsi a Duniya, (Global Gender Gap) a kan wasu bangarori hudu, harkar lafiya, da ilimi, tattalin arziki da kuma siyasa.

A shekarar 2016, kasashen da suke da kankantar daidaiton jinsi, da suka hada da Iceland, da Finland, da Norway, su ne suka fi son samun mata su shiga harkar siyasa. Hakan ya nuna cewa mata za su fi kawo ci gaba a kasashe.

Sai dai mawuyacin abu ne a samu alaka tsakanin mata shugabanni da kuma samun ingantacciyar rayuwa a kan takwarorinsu mata. Sai dai ba duka ba ne saboda an samu nuna rashin bambanci a karnin da suka shude na kusan ko wacce kasa, ba tare da la'akari da samun shugaba mace ba.

Har ila yau, saboda yawancin matan ko dai an zabesu ne a baya-bayan nan ko kuma suna kan mukaminsu na lokaci kadan, zai yi wahala a auna wani tasirin tsare-tsarensu.

A bangare guda kuma, wadannan hujjojin sun nuna cewa matan da suka samu nasara suna kara saka wa matan kasarsu karsashi, har ila yau kuma kasarsu na matukar son samun ingantacciyar rayuwar mata.