'Kada ta kashe wata tsohuwa' a Australia

Anne Cameron Hakkin mallakar hoto Queensland Police
Image caption Tun ranar Talata ne Anne ta bata

'Yan sanda wadanda suke neman wata mata a Australiya sun ce da alama kada ce ta kashe ta.

An kawo rahoto cewa ana cigiyar wata mata Anne Cameron mai shekara 79 da ta ke zama a wani gidan kula da tsofaffi kusa da garin Queensland na Port Douglas a ranar Talata.

An samu kaya da sandar dogarawa mai dauke da sunanta kusa da bakin kogi, kuma matar tana fama da ciwon mantuwa.

A ranar Juma'a 'yan sanda sun samu ragowar bangarorin jikin mutum, kuma suna zaton cewa na Anne Cameron ne.

Mataimakin shugaban 'yan sanda Ed Lukin ya ce: ''Muna zaton cewa da alama kada ce ta kai mata hari.''

''Za a gudanar da bincike don a gano ko bangarorin jikin mutum din da aka gano na Anne Cameron ne."

'Yan sanda suna zargin cewa kadar ta kai wa Anne Cameron hari ne a lokacin da ta shiga cikin wani jeji wanda yake da nisan kilomita biyu daga gidan kula da tsofaffin da take.''

Wasu kafofin yada labarai sun ruwaito cewa, ''Ta koma gidan kula da tsofaffin ne don ta zauna cikin sa'o'inta.''

Jami'an da ke kula da dabbobin daji za su saka tarkon kama kada a yankin da aka ga gawar.

Hare-haren da kada ke yawan kai wa sun yi sanadaiyyar mutuwar mutum tara a Queensland tun shekarar 1985, ciki har da wani masunci a watan Maris din da ya gabata.

Labarai masu alaka