Boko Haram: An sallami mutum 468 da ake zargi

Boko Haram Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Amnesty International sun yi kira da ayi wa wadanda ake zargin adalci

Wata babbar kotu mai zama a garin Kainji da ke jihar Niger a arewacin Najeriya, ta yanke wa wasu mayakan Boko Haram 45 hukuncin daurin daga tsakanin shekara 3 zuwa 31, bayan ta same su da laifi a shari'ar da aka yi wa wasu 'yan kungiyar su 575 .

A wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Juma'a, ministan yada labarai da al'adu na kasar, Alhaji Lai Mohammed, ya ce kotun ta wanke mutum 468 wadanda ba a samu da laifi ba.

An yi watsi da shari'ar mutum 34, yayin da aka ajiye mutum 28 a gidan wakafi domin a yi musu shari'a a Abuja da Minna.

Kotun ta bayar da umarnin cewa a yi wa mutum 468 da ta wanke din hororwa na sauya tunani kafin a mika su ga gwamantocin jihohinsu.

An fara hukuncin shari'ar ta gama gari ne bayan kotu ta ajiye mutum 1,669 da ake zargi da kasancewa 'yan Boko Haram na tsawon kwana 90 a gidan wakafi.

Kuma kotun ta bayar da umarnin cewa a gurfanar da su cikin wannan lokacin ko kuma a sake su ba tare da sharadi ba.

Kotun ta daga shari'ar da ake yi wa ragowar wadanda ake zargi da kasancewa 'yan Boko Haram din zuwa watan Janairun shekarar 2018.

Labarai masu alaka