Mata sun yi kira da a kauracewa shafin Twitter

Shafin Twitter Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shafin Twitter na da dumbin mabiya

Jaruman fina-finai na Hollywood da masu fafitika sun yi kira don a kauracewa shafin sada zumunta na Twitter, bayan da kamfanin Twitter ya dakatar da Rose McGowan, wata jarumar fim wanda ta zargi Harvey Weinstein wani mai shirya fina-finai da yi mata fiyade.

Shafin na Twitter ya ce ta karya dokokinsu a cikin wadansu sakonni da ta wallafa a shafinta na Twitter.

Masu goyon bayan Rose McGowan sun yi amanna cewa, an hana ta magana ne don tana amfani da shafin wajen yin korafi a kan Mista Wenstein da ma sauran wasu fitattun mutane, wadanda ta ce sun san abin da yake mata na cin zarafi amma ba su yi komai a kai ba.

Mista Weinstein ya karyata duk wani zargin cin zarafi.

Maudu'in da aka kirkiro don yada batun mai taken 'Women Boycott Twitter' wato 'Mata su kautracewa Twitter' ya ja hankalin mutane sosai, duk da cewa mata da dama sun kauracewa amfani da shafin.

Labarai masu alaka