Shugaba Buhari ya gana da yara masoyansa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da yaran Hakkin mallakar hoto Nigeria Presidency
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya yi matukar farin cikin ganawa da yaran a fadarsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin wadansu yara uku mata kanana wadanda ake cewa masoyan shugaban ne a fadarsa da ke Abuja.

Nicole Benson 'yar shekara 12 wadda ta fito daga jihar Legas da Maya Jamal 'yar shekara uku wadda take zaune a Abuja da kuma Aisha Gebbi mai shekara 10 wadda ta fito daga jihar Bauchi sun isa fadar ne tare da rakiyar iyayensu.

Hakkin mallakar hoto Twitter/Bashir Ahmad
Image caption Maya mai shekara uku, ta isa fadar shugaban ne tare da mahaifinta

Yaran sun kwashe kimanin minti 30 a fadar shugaban kasar.

Kafofin yada labaran kasar sun sha ruwaito labarin daya daga cikin yaran wato Nicole a lokacin zaben shekarar 2015, inda suka ce ta taba tallafa wa shugaban da kudin abincinta.

Ba kasafai dai ake ganin shugaban yana ganawa da kananan yara ba.

Karanta karin wadansu labaran masu kayatarwa

Hakkin mallakar hoto Nigeria Presidency
Image caption Aisha 'yar shekara 10 tana karbar kyautar daga hannun Shugaba Buhari
Hakkin mallakar hoto Nigeria Presidency
Image caption Nicole 'yar shekara 12 ta taba tallafa wa shugaban da kudi yayin da yake yakin neman zabe a shekarar 2015

Labarai masu alaka