Mata na cikin hadari a Alkahira babban birnin Masar

Masu rajin kare hakkin mata sun ce mata na rayuwa cikin wahala a Alkahira
Image caption Masu rajin kare hakkin mata sun ce mata na rayuwa cikin wahala a Alkahira

An bayyana Alkahira babban birnin Masar a matsayin birnin da ya fi hadari ga mata.

An gano haka ne daga kuri'ar jin ra'ayoyin jama'ar duniya ta farko da aka yi, a kan yadda mata suke rayuwa a cikin birane da ke da mazauna fiye da miliyan 10.

An gudanar da binciken ne a birane 19 inda aka yi wa kwararru kan harkar mata tambayoyi kan kariyar da ake basu kan batun da ya shafi cin zarafi.

Kuri'ar ta bayyana Landan a matsayin birnin da mata ba sa fuskantar takura, kuma Tokyo da Paris na binsa a baya.

Magajin garin Landan Sadiq Khan ya ce mata na tasiri sosai a fannoni da dama a Landan, ciki har da ma'aikatun gwamnati da kasuwanci da kuma siyasa.

Masu rajin kare hakkin mata a Alkahira sun dora alhaki kan wasu al'adu da aka dade ana amfani da su dagane da wariyar da ake nuna masu.

Haka kuma babu isassun asibitoci masu inganci na mata, kuma suna fuskantar matsalar rashin kudi da kuma ilimi.

Birnin Karachi na Pakistan da Kinshasa na Jamhuriyar Dimokradiyar Congo da Delhi na India sune suke bayan birnin Alkahira a binciken da gidauniyar Thomson Reuters ta yi.