Ba ruwana da ko wacce Jam'iyya - Obasanjo

Cif Obasanjo ya ce abun da ya sa gaba shi ne yadda Najeriya za ta ci gaba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Cif Obasanjo ya ce abun da ya sa gaba shi ne yadda Najeriya za ta ci gaba

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya ce ya daina shiga dumu-dumu harkar duk wata jam'iyyar siyasa a kasar.

Cif Obasanjo ya shaida wa manema labarai hakan ne jim kadan bayan ganawa da shugaban jam'iyyar PDP Sanata Ahmed Markafi da suka ziyarce shi a Abeokuta.

Tsohon shugaban kasar ya ce babban abun da ya sa a gaba yanzu shi ne ganin yadda Najeriya za ta ci gaba yana mai cewa: "batun ci gaban Najeriya mutu ka raba ne".

Ya kara da cewa Najeriya tana bukatar babbar jam'iyya mai mulki da kuma babbar jam'iyyar adawa da za ta rika sa ido kan yadda gwamnati ke tafiya don ci gaban dimokradiyya.

Da yake tsokaci game da ganawarsa da shugabannin Jam'iyyar PDP da suka ziyarce shi, Cif Obasanjo ya ce ya shaida wa Sanata Makarfi cewa a baya ya yi PDP amma yanzu shi ba ya wata jam'iyyar inda ya jaddada cewa shi ba ya yin amai ya dawo ya lashe.

Labarai masu alaka