Buhari ya caccaki gwamnoni kan albashi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya nuna damuwa akan yadda ake cigaba da samun korafe korafe kan batun albashin ma'aikata a jihohin kasar.

Shugaban ya ce abin takaice ne cewa wasu jihohi sun kasa sauke nauyin da ke kansu na biyan aklbashin ma'aikata duk da makudan kudin da gwamnatinsa ta baiwa jihohin domin su biya ma'aikata hakkokinsu.

Shugaba Buhari ya ce rabin na daure masa kai yadda ma'aikata a jihohi ke iya daukan dawainiyar iyalansu su ciyar da su, kana su biya musu kudin makaranta duk da cewa gwamnonin basa biyansu albashi a kan lokaci.

Ya kuma ce da mamaki gwamna ya iya barci duk da cewa bai biya ma'aikata albashinsu ba na tsawon watanni.

Ya ce da bukatar a sake lale domin ganin an warware matsalar.

Amma shugaban kungiyar gwamnonin, Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ya ce lamarin ya sha karfin gwamnonin ne saboda yawancinsu sun gaji matsalolin ne daga hannun tsofaffin gwamnoni a shekarar 2015.

Wannan matsalar ta rashin biyan albashi tayi kamari a Najeriya, a inda a wasu lokutan har ta kan kashe auren wadanda lamarin ya shafa.

Masu sharhi na ganin cewa duk da wadannan matsalolin, gwamnonin kasar basu daina gudanar da rayuwa irin ta kasaita ba da kuma almubazzaranci da dukiyar al'umma.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kar Buhari ya sake bai wa gwamnoni Kudi

Wasu ma'aikata da wakilinmu, Nura Muhammad Ringim, ya yi zanta da su a Kaduna sun yaba wa kalaman shugaban kasar, kuma sun yi tir da rashin biyan albashin da wasu gwamnonin kasar suka yi.

Daya daga ma'aikatan gwamnatin ya ce: " Akwai gwamnonin da shi Shugaban kasa ya biya su wadannan kudaden da yake ba su. Su kuma sun bi wata hanay da kudin. A gaskiya bai dace ba ko alama, kwata-kwata bai dace ba. "

Wani ma'aikacin kuma cewa yayi bai kamata Buhari ya sake bai wa gwamnonin kudi ba. Da aka tambaye shi da me za su biya ma'ikata, sai ya ce: "Za su yi farauta. Saboda a nan yanzu haka a jiha babu gwamnan da ba ya karbar harajin da zai iya rike ma'aikatunsa ba. To, ina suke kai wannan kudin?

Saurari hirar Nura Muhammad Ringim da ma'aiakatan:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kar Buhari ya sake bai wa gwamnoni kudi, in ji wasu ma'aikata

Labarai masu alaka