Somaliya na neman agajin jini

An kasa tantance da dama daga cikin mutanen da suka hallaka a cikin harin Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kasa tantance da dama daga cikin mutanen da suka hallaka a cikin harin

Somaliya ta yi kira ga kasashen duniya akan su taimaka mata da agajin jini domin kula da wadanda suka ji raunuka a harin bam da aka kai da wata babbar mota a Mogadishu babban birnin kasar a ranar Asabar, wanda ya hallaka mutum 281.

Ministan yadda labarai na kasar Abdirahman Osman ya shedawa BBC cewa watakila adadin wadanda suka rasu ya sake karuwa kuma ana bukatar karin taimako.

Ya ce mutum fiye da 300 ne suka ji raunuka a harin ta'aadanci mafi muni da aka kai a kasar a cikin shekara goma kuma kawo yanzu akwai gawarwwakin mutane a karkashin gine ginen da suka ruguje.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana yi wa wadanda suka ji raunuka jiny

Turkiya da Djibouti sun tura da ma'aikatan agaji zuwa kasar a ranar Litini kuma jirgin sama sojin Turkiya ya wuce da wasu mutane 40 da suka ji raunuka zuwa kasar domin a yi mu su magani.

Kasar Kenya makobciya ta nuna anniyar kwashe wasu da suka ji raunuka zuwa birnin Nairobi da jirgin sama domin a yi mu su magana.Haka daruruwan mutane sun bada gajin jini