Kar Buhari ya sake bai wa gwamnoni kudi
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kar Buhari ya sake bai wa gwamnoni kudi, in ji wasu ma'aikata

Wasu ma'aikata da BBC ta zanta da su kan caccakar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa gwamnonin kasar game da rashin biyan albashi, sun goyi bayan kalaman shugaban Najeriyar kuma sun nemi gwamnoni da 'yan majalisu su bai wa shugaban kasar hadin kai.