Yadda ake rawa da gawarwaki a Madagascar
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kun san kasar da ake tono gawarwaki a yi rawa da su?

Zai zamo wani abin al'ajabi ga wasu al'ummun idan suka ji labarin yadda a wasu sassa na duniya mutane ke tono gawarwakin 'yan uwansu tare da cashe rawa da gawarwakin.

A tsaunukan Madagaska da ke nahiyar Afirka, wannan tsohuwar al'ada ce wadda aka fi sani da "juya gawarwaki"- kuma ana shirya gagarumin biki ne don tono gawarwaki da yin rawa da su.