Wadanda suka yi belin Nnamdi Kanu na tsaka mai wuya

A watan Afrilu 2017 ne aka bayar da Nnamdi Kanu beli bayan ya shafe wata 18 a tsare. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A watan Afrilu 2017 ne aka bayar da Nnamdi Kanu beli bayan ya shafe wata 18 a tsare.

A Najeriya, mutanen uku ciki har da wani dan Majalisar dattawan kasar da suka yi belin Shugaban kungiyar 'yan a-ware ta Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu na tsaka mai wuya.

Hakan ya biyo bayan rashin bayyanar sa a gaban kotu ranar Talata, inda mai shari'a Binta Nyako ta bada umurnin su kawo shi.

Sanata Enyinnaya Abaribe da Immanuel Madu da kuma Torchokwu Uchendu sune suka yi belin Mr Kanu wanda ake yi wa shari'a a Kotun tarayya da ke Abuja kan zargin cin amanar kasa.

Shi dai lauyan Mr Kanu, Mr Ifeanyi Ejiofor ya shaida wa kotu cewa bai san inda wanda yake kare wa yake ba.

Mai shari'a Binta Nyako ta ce matukar wadanda suka tsayawa Mr Kanu suka kasa kawo shi gaban kotun, za su rasa Naira miliyan 100 da suka ajiye cikin sharuddan belin.

Me ake bukata wadanda suka tsayawa Kanu beli su kawo?

  • Dole sai sun kawo shi
  • Ko a tsare su
  • Ko kuma su rasa Naira miliyan 100 da kowannensu ya ajiye na beli

Ga dai cikakken bayani da Barista Muhammad Modibbo Bakare, masanin harkokin shari'a a Najeriyar ya yi wa Haruna Shehu Tangaza kan zabin da mutanen uku ke da shi.

Sai ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraro:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hanyar da ta rage wa masu belin Nnamdi Kanu

Labarai masu alaka