Ta ya ya Saudiyya za ta hana yada Hadisan karya?

Malamai a Saudiyya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Malaman saudiyya na cikin manyan Malamai daga sassan duniya za su rika sa ido kan wannan aikin

Gwamnatin Saudiyya za ta kafa wata sabuwar cibiyar addini wacce za ta hana masu tsattsauran ra'ayin Musulunci da kuma 'yan ta'adda jirkita wasu Hadisai domin aikata danyen aiki.

Mahukunta a kasar sun ce ''yan ta'adda" na gurbata fassarar hadisan Annabi Muhammad (SAW), domin kafa hujja da su wajen munanan ayyukan da suke yi.

Sarki Salman ne ya sanya hannu kan wani kudurin dokar wanda ya bayar da damar kafa wannan cibiya.

Kuma jami'an sun ce cibiyar za ta kasance ne a birnin Madinah mai tsarki.

Za a dauki Malamai kuma masana addinin Musulunci daga sassan duniya daban daban wadanda za su jagoranci cibiyar.

Za kuma su rinka aiki tukuru domin zakulo da kawar da duk wani Hadisi da ke da alamun kage ko wanda aka sauyawa ma'ana domin kafa hujjojin tayar da fitinah.

An dade ana zargin kungiyoyin masu tayar da kayar baya kamar su Al'Qaeeda da IS wajen sauya ma'anar ayoyin Al'Kur'ani da Hadisai domin kafa hujja kan ta'asar da suke aikatawa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar IS ta rasa mafi yawan yankunan da ta kama a kasashen Iraki da Syria

Wannan mataki na zuwa ne watanni kadan bayan ziyarar da Shugaban Amurka Donald Trump ya kai kasar ta Saudiyya, inda mahukunta suka yi masa alkawarin kawo gyara a yadda suke tunkarar batun tsattsauran ra'ayi.

Wasu dai na zargin cewa wadannan sauye-sauye ba za su rasa nasaba da matsin lambar da Amurka ke wa kasar ba, na ganin ta sauya yadda take tafiyar da al'amuranta na addini.

Sai dai jami'an Saudiyya sun musanta irin wadannan zarge-zarge.

Akwai dubban Hadisai da Annabi Muhammad (SAW) ya bari, da musulmai ke ci gaba da amfani da su wajen kara fahimtar addinin.

Baya ga Al'Qur'ani mai girma, Hadisin Annabi (SAW) shi ne mafi muhimmanci a tsarin shari'ar addinin Islama, amma ana samun wasu Hadisan da ake jirkita ma'anarsu, ko kuma wadanda ba su da asali.

A don haka ne Saudiyya da sauran kasashen musulmi suka ci gaba da nuna damuwa.

Sheikh Abdulrazak Ibrahim, Limamin Masallaci Unguwar Seven Sisters a arewacin London, ya ce dokar za ta iya yin tasiri sosai.

Ya shaida wa BBC cewa "Tana da muhimmanci" ganin yadda aka ce malaman da za su kula da cibiyar za su fito ne daga kasashen Musulmi da dama.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sarki Salman ya ce manyan Malamai ne daga sassan duniya za su rika sa ido

Sai nan gaba ne za a bayyana cikakken tsarin da za a bi wurin aiwatar da cibiyar da kuma lokacin da za ta fara aiki.

Labarai masu alaka