Mutum 4 sun hallaka a Togo

Masu zanga zangar sun taho-mu-gama da 'yan sanda Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu zanga zangar sun taho-mu-gama da 'yan sanda

Mutum 4 suka hallaka a Togo a zanga zangar nuna rashin amincewa da gwamnati na baya baya nan .

Masu zanga zangar sun yi artabu da jamian tsaro a Lome, babban birnin kasar da kuma garin Sokode, inda suka kafa shigaye a kan tituna.

Yan sanda sun harba hayaki ma sa hawaye domin tawartsa masu zanga zangar.

Mace macen sune alamari na baya baya nan kan gangamin da ake yi domin nuna rashin amicewa da shirin shugaba Faure Gnassingbe na yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.

Masu zanga zangar na son ya sauka daga mulki idan wa'adinsa ya zo karshe a shekarar 2020 kuma kada ya nemi karin wa'adi biyu akan karagar mulki.