Kamfanin man kara hasken fata na Nivea na tsaka mai wuya a Afirka

Man Nivea Hakkin mallakar hoto Folaranmi Twitter

Babban kamfanin man shafawa na Nivea yana fuskantar kalubale bayan da ya fitar da wani tallan man shafawa mai kara hasken fata a Afirka ta yamma.

An haska tallar man na talabijin an kuma sanya a allunan talla na kan titi, inda aka yi masa lakabi da "farar fata ta ainihi," a Najeriya da Ghana da kamaru da kuma Senegal.

An kuma yi amfani da hoton wadda ta taba zama sarauniyar kyau ta Najeriya, Omowunmi Akinnifesi a tallar.

Wata mai tallan kayan kawa Munroe Bergdorf, wacce aka sallama kwanan nan daga wani talla na kamfanin L'oreal bayan da ta yi magana a kan wariyar launin fata a Amurka, na daya daga cikin wadanda su ka soki tallar ta Nivea, wanda ta sa a shafinta na Instagram.

Duk da mutane da yawa sun nuna cewa man shafawar ba sabon fitowa ba ne, ya zama abin cece-kuce a kan shafukan sada zumunta.

Kamfanin Nivea din ya nemi afuwa kan wannan abu, inda ya shaida wa BBC cewa ba su yi hakan da nufin su bata wa abokan huldarsu rai ba.

Ko a baya-bayan nan ma mutane sun yi ta sukar wani tallan kamfanin Dove da ya nuna alamar wariyar launin fata.

Mai tallan kayan kawar da ta fito a tallar ta Dove wacce 'yar asalin Najeriya ce kuma 'yar kasar Amurka, Lola Ogunyemi, ta fito ta tofa albarkacin bakinta kuma ta kare kanta a game da tallar inda ta ce mutane sun yi wa tallar mummunar fahimta ne.

Hakkin mallakar hoto Getty Images