Gurbatar muhalli ya fi kashe talakawa — Rahoto

Mutane na mutuwa kafin tsufansu saboda gurbatar yanayi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gurbacewar iska ita ce sababi mafi girma da ya fi kashe mutane in ji rahoton

Wani nazari ya yi kiyasin cewa gurbatar muhalli ya haddasa mutuwar mutum miliyan 9 kafin tsufansu cikin shekara ta 2015 a duniya.

Nazarin ya kalailaice bayanai na cutukan da ke da nasaba da gurbatar yanayi irinsu ciwon zuciya da shanyewar barin jiki.

Alkaluman mace-macen wuri sun dauki kaso kimanin 16 cikin 100 na duk mutuwar da aka yi a fadin duniya.

Daya daga masu binciken, Richard Fuller, ya ce talakawa sun fi saurin mutuwa kafin karewar karfinsu saboda gurbacewar muhalli.

Kusan duk mace-macen da ake samu kafin tsufa, na faruwa ne a kasashen da ake da karanci ko matsaikaicin samu na duniya.

Kasashen Bangladesh da Somalia su ne kasashen da aka fi samun irin wannan matsalar a cewar nazarin, yayin da kasashen Brunei da Sweden kuma su ne ba a fiye samun mace-mace sakamakon gurbatar yanayi ba.

Yawancin mace-macen da ake samu wadanda ke da nasaba da gurbatar muhalli sun hadar da ciwon zuciya da shanyewar barin jiki da kuma cutar kansa ko dajin huhu.

Shi ma, Farfesa Philip Landrigan da ke cikin masu binciken ya ce gurbacewar yanayi ba wai kalubale ne da ya shafi muhalli ba, wata gagarumar barazana ce da ta shafi lafiya da kuma walwalar al'umma.

Binciken ya ce daga cikin abubuwan da ke janyo gurbacewar muhallin sun hada da isakar gas din da ake shaka a kan tituna da kuma hayakin itace ko gawayin da ake konawa a cikin gidaje.

Binciken ya ce baya ga wadannan abubuwa da ke taimakawa wajen gurbatar yanayi, gurbacewar ruwa ma na da matukar illa ta yadda ke janyo mutuwar mutane da dama.

Haka kuma, binciken ya ce ana yawan samun mace-mace sakamakon gurbatar muhalli a kasashen da tattalin arzikin kasarsu ke bunkasa cikin sauri kamar India da China, inda aka sanya su a matsayi na 16 a cikin jerin kasashen da ake samun mutuwa sakamakon gurbatar yanayi.

Binciken ya ce kasashe kamar Birtaniya da Amurka da ma na Tarayyar Turai ciki har da Jamus da Faransa da Italiya da Spaniya da kuma Denmark, ana samun irin wannan matsala, sai dai su nasu bai kai yawan na kasashe masu tasowa da kuma wadanda ke fama da talauci ba.

Rahoton ya ce, da gurbacewar yanayi da fatara da rashin ingantacciyar lafiya da kuma rashin daidaito a tsakanin al'umma na da matukar alaka da juna.