'Wane ɗan Boko Haram ne ya taba karatu a Saudiyya?'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Jawabin Dakta Sani Rijiyar Lemo kan cewa Saudiyya ba ta goyon bayan ta'addanci

Ku latsa alamar lasifikar nan ta sama don sauraron jawabin Dr. Muhammadu Sani Umar Rijiyar Lemo kan wannan batu.

Wani malamin addinin musulunci a Najeriya ya kalubalanci ikirarin cewa kasar Saudiyya na koyar da fannonin ilmi da ke rura wutar tsaurin ra'ayin addinin musulunci a duniya.

Dr. Muhammadu Sani Umar Rijiyar Lemo wanda malami ne a Jami'ar Bayero Kano, ya kuma yi karatun digirinsa na farko har zuwa na uku a Saudiyya, ya ce da gaskiya ne wannan zargi to da yanzu duniyar ma ba za ta zaunu ba saboda yawan masu zafin ra'ayi.

Dr Sani ya yi ikirarin cewa Allah ya yi yawa da daliban da kasar ta yaye a duniya, kuma da tsattsauran ra'ayin addini suka koya "da yanzu duk mu ma mun zama 'yan ta'adda".

"Muna nan irinmu ba iyaka. Ba na jin akwai wata kasa da ta yaye dalibai na ilmi wadanda suke karantarwa kamar Saudiyya, in ji shi."

Ya ce yanzu idan ka dubi wadanda ake fama da su a nan kasar ('Yan Boko Haram), dalibi nawa ne aka ce maka daga Saudiyya yake? Wane ne a cikinsu ya je Saudiyya ya yi karatu?

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Dr Sani Rijiyar Lemo yana ganin kuskure ne alakanta yadda ake karantar da addinin Musulunci a Saudiyya da yaduwar tsattsaurar ra'ayin addini a duniya

Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo na wannan jawabi yayin zantawa ta musammam da BBC game da yunkurin hukumomin Saudiyya na bude wata cibiya da za ta rika tantance sahihan hadisan Annabi Muhammadu (S.A.W), don hana masu tsaurin ra'ayi jirkita ma'anoninsu.

Ya ce kudurin bude wannan cibiya ya samo asali ne daga kiraye-kirayen malamai da masana kimanin tsawon shekara 20 da ta gabata don fadada wannan cibiya.

"Akwai Markazutu Hikmatu Sunnan Nabawiyya wanda sashe ne a cibiyar Mujamma'ana Malik Fahad da hadin gwiwar Jami'ar Islamiyya a kasar Saudiyya wanda ya faro wannan gagarumin aiki tun wancan lokaci."

A cewarsa: "Jingina abin da wata matsin lambar Kasashen Yamma ga wannan yunkuri na Saudiyya, wata muguwar fassara ce da wasu ke yi, amma kwata-kwata babu wannan abin ko kadan," in ji shi.

Dr. Sani Rijiyar Lemo ya ce irin aikin da wannan cibiya za ta yi, zai taimaka wajen fito da ma'anonin hadisan Annabi daga malaman farko.

"Bukhari da Muslim da sauran manyan litattafan hadisai suna da sharhin da malamai suka yi musu tun sama da shekara dubu."

Ya ce hidima ta ilmi ba ta da alaka da wani wanda zai zo yana ta barna a bankasa, da sunan addini, maimakon haka ma ita ce za ta rushe abubuwan da yake fada da ba na gaskiya ba.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo ya ce 'yan Boko Haram a Najeriya suka samu tsattsauran ra'ayinsu, don kuwa ba su taba zuwa Saudiyya karatu ba

Labarai masu alaka