Nigeria: Atiku ya yaba wa Shugaba Buhari

Atiku ABubakar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Atiku dai ya caccaki Buhari a baya-bayan kan yadda yake tafiyar da mulkinsa

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar, ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari a kan umarnin da ya bayar na biyan jami'an tsaron da suka yi yakin Biafra wadanda aka yi wa afuwa, hakkokinsu na fansho.

Atiku Abubakar wanda ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter ya ce, abin da Shugaba Buharin ya yi na nuna hadin kan Najeriya.

A ranar Laraba ne Shugaba Buhari ya amince da biyan fanshon ga jami'an 'yan sandan da gwamnatin Najeriya ta yi wa afuwa tun a shekarar 2000 lokacin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo.

Wadannan 'yan sanda sun yi aiki ne a 'haramtacciyar' kasar Biafra a lokacin yakin basasar Najeriya da aka shafe watanni 30 ana yi.

Sai dai tun bayan da aka yi musu afuwar ba a biya su komai daga cikin kudaden fanshonsu ba.

A wata sanarwa da wata hukuma wadda ke kula da biyan fanshon ta fitar ta ce, za a biya mutum 162 yayin da mutum 57 kuma iyalansu ne za su karba a madadinsu a biyan farko da za a yi.

Hukumar ta kuma ce za a fara biyan farkon ne ranar Juma'a 20 ga watan Oktobar nan a birnin Enugu da ke Kudancin Najeriya.

Sai dai watakila wannan yabo da Atiku Abubakar ya yi wa Shugaba Buhari ya zo wa wasu da mamaki, ganin cewa a baya-bayan ya caccaki gwamnatin Buharin kan al'amura da dama da suka hada da korafin da ya yi na watsi da shi da aka yi a tafiyar da harkokin gwamnatin.

Labarai masu alaka